Pep Guardiola mai horas da kungiyar kwallon kafa ta manchester City ya ce “babu kalmomi da za su taimaka” wajen rage radadin kawar da Manchester City da aka yi daga gasar zakarun Turai yayin da ya sake mayar da hankali kan kalubalantar gasar Premier.
‘Yan mintuna kadan ne City ta samu tikitin zuwa wasan karshe da Liverpool kafin Real Madrid ta yi fafatawa mai ban mamaki a Bernabeu ranar Laraba, wadda ta haifar da rashin nasara ga Man City din.
Real ta zura kwallaye biyu a cikin dakika na karshe na lokacin da aka saba, kuma daga karshe ta samu nasara a wasan da ci 3-1 bayan karin lokaci, inda aka tashi wasan dab da na kusa da karshe da ci 6-5.
Da aka tambaye shi a jiya Juma’a abin da ya ce wa ‘yan wasansa, Guardiola ya shaida wa manema labarai: “Ba mu yi magana ba.
Babu kalmomi da za su iya taimakon halin da muke ciki.
“Tambaya ce ta lokaci, yi ƙoƙarin yin barci da tunanin abubuwan da ake hari. Gobe za mu yi magana.”
A yanzu dole ne kocin City ya dauko mutanensa domin buga gasar Premier, dake tafe nan gaba.
City, wacce ke jagorantar Liverpool da maki daya kacal saura wasanni hudu, za ta karbi bakuncin Newcastle a tsakiyar tebur a ranar Lahadi, kwana guda bayan kungiyar Jurgen Klopp da Tottenham.
Guardiola, wanda ya lashe kofunan gasar zakarun Turai sau biyu a lokacin da yake horar da Barcelona, ya ce Real ta cancanci nasarar da ta samu, amma ya sha alwashin City ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen cimma burinta na gasar zakarun Turai.
Comments 1