Gawar Sani Ɗangote, Ƙanen Fitaccen Attajiri wanda yafi kowa kuɗi a Afrika Alhaji Aliko Ɗangote, an sanya zata iso Najeriya a ranar Talata, daga Ƙasar Amurka.
Sani, mataimakin Kamfanin Rukunin Ɗangote, ya rasu a ranar Lahadi biyo bayan gajeruwar rashin lafiya a Amurka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Jihar Kano Ya Aike Da Sakon Ta’aziyyar Sa Zuwa Ga Dangote bisa rasuwar dan uwa
Wata majiya daga iyalan tace “sani Ɗangote ya kasance yana fama da Ciwon daji, kuma ya tafi ƙasar Amurka domin neman maganin cutar, amma yadda Allah yaso, ya rasu yana da shekaru 61.
“A taƙaice, iyalan Ɗangote suna jin wannan mutuwa, amma sun amshe ta da imanin haka Allah yaso.
Sani ya rayu da Mahaifiyar sa, Mata, da ƴaƴa 8 da yayye da ƙanne.
Tun bayan Labarin rasuwar Sani, Masu jaje suke ta zuwa iyalan Ɗangote a unguwar Koki dake garin Kano.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, sallah jana’izar zata gudana a gidan Aliko Ɗangote dake GRA ta Nasarawa.
A lokacin da wakilin Jaridar Daily Trust ta ziyarci unguwar Koki gidan Marigayin, an lura dacewa ciyarwar da ake yi ta ɗaruruwan mutane na gudana kamar yadda aka saba.
Kafin rasuwar sa, Sani Ɗangote ya kasance mataimakin Shugaban Rukunin Ɗangote, kuma Mataimakin Shugaban Ƙungiyar AGAPA, kuma shugaban Polo karo na biyu na Jahar Lagos, kuma ya kasance yana cikin ƙungiyoyi da dama.