Ministan shari’a, kuma babban mai shari’a na gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, SAN a ranar Juma’a ya raba kayayyakin abinci ga mutum sama da dubu biyar a jihar Kebbi.
Dr Umar Gwandu, mai tallafawa ministan akan harkokin kafafen watsa labarai, shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ministan ya raba tallafin abinci ne ta hannun wata kungiya da ba na gwamnati ba da ministan ya samar mai suna ‘Khadimiyya for Justice and Development Initiative.’
Ya ce wannan tallafin yana daya daga cikin abubuwan da ministan ya yi wajen tallafawa marasa karfi a wani mataki na manufofin gwamnatin Buhari na taimakon al’umma.