Mahaifiyar Mawallafin Jaridar Dimokuraɗiyya Hajiya Hauwa’u Salihu na Kwance a Asibiti ba ta da Lafiya, inda take matukar buƙatar addu’ar al’umma baki daya.
Haruna Khalifa, Mawallafin Jaridar shi ne ya nemi haka a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, inda ya ce duk da tana samun kulawar Likitoci, amma yana mai amfani da wannan lokaci da kuma wannan wata na Ramadana da ake ciki yana bidar addu’o’i daga al’umma baki daya da nufin Allah ya bai wa mahaifiyarsa lafiya, sannan “Da Fatan Allah ya tashi Kafaɗunta.” Inji sanarwar.