Hajiya Lami foundation da ke garin Samaru a karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna sun bayar da tallafi ga mutane a kalla 200.
Cibiyar dai kamar yadda bincike ya nuna, mahaifiyar Honorabul Yusuf Shaka, dan takarar kujerar karamar hukumar Sabon Gari ne a shekarun da suka gabata ta kafa ta tare da gudummawar yaranta da suke aiki a wurare daban-daban wanda kuma suka yi fice wajen taimako a duk inda suke gida da waje.
Kuma bincike ya tabbatar da cewa gidauniyar an kafa ta ne don taimakawa marasa galihu musamman a bangarori daban-daban na rayuwa ciki harda bangaren kiwon lafiya.
Tuni wannan gidauniyar ta sami yabo mai yawa wajan jama’ar karamar hukumar Sabon Gari bisa yadda suke gudanar da aikinsu na tallafawa al’umma lokaci bayan lokaci.
A wannan lokacin ma gidauniyar ba ta yi kasa a guiwa ba wajen bayar da tallafin kamar yadda ta saba musamman ganin yadda mutane suka galabaita a sanadiyar annobar cutar korona kamar yadda wakilinmu ya ruwaito mana.
Hajiya Lami Foundation ta baiwa mutane 200 tallafin magunguna tare da yi musu gwaje-gwaje akan matsaloli mabambanta.
Daga cikin matsaloli sun hada da zazzabin cizon sauro da matsalar hawan jini sai ciwon suga da dai sauran cutuka dake addabar jama’a a yanzun Kuma a wannan lokacin.
Gamayyar likitoci ne daga cibiyoyin aikin lafiya a Kaduna da Zariya suka kasance a wajen bayar da tallafin Inda kungiyar (Red cross) suka bayar da kariya ga marasa lafiya da masu aikin lafiyar.
Ganau sun tabbatar da cewa babu wata Gidauniya a fadin jihar Kaduna dake gudanar da aikin taimakon talaka a bangaren kiwon lafiya kamar yadda Gidauniyar Hajiya Lami ke gudanarwa a wannan lokacin .
Ganau sun kara bayyana cewa, ko yanzu in har mara lafiya na da takardun da suka nuna cewa likitoci suka rubuta mashi musamman ABUTH to duk maganin da aka rubuta mashi mara lafiyar, to Gidauniyar za ta nemo maganin komin tsadarsa su ba mara lafiyar kyauta ba sisin kobo.
Malama Rabi Ibrahim mai fama da ciwon hawan jini na daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin, a yayin da take hira ga manema labarai bayan an yi mata gwaji tuni ta nuna jindadinta tare da yiwa yara da jikokin Hajiya Lami tare da fatan Allah ya biya musu bukatar su duniya da lahira.
Dakta Muhammad na daya daga cikin likitoci da suka duba mutanen da aka gwada, shima ya nuna Jindadinsa bisa yadda aka ba su goyan baya har suka duba mutane 200 ba tare da wani hatsaniya ba, kuma ya yi fatan alheri ga dukkan ‘ya’yan Hajiya Lami da suke bayar da gudummawarsu don taimakawa al’umma.
Alhaji Imran shi ne shugaban shiyya na kungiyar ‘Red cross) a karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna kuma shi ya jagoranci kungiyar ta su, shima ya yabawa ayarin likitoci da masu bada maganinsu (pharmacist) da jama’ar garin Samaru baki daya bisa hadin kai da suka bayar yadda aka fara lafiya haka aka gama lafiya. .
Hajiya Lami, Mahaifiyar Honorabul Yusuf Shaka ita ce uwa ga Gidauniyar kuma karkashinta ne gidauniyar take gudanar da aiki a na ta kalaman lokacin da aka kammala bayar da tallafin ga Jama’a ta ce; “Ina godiya ga Allah madaukakin Sarki Kuma na roki Allah ya karawa Annabi daraja tare da Sahabbansa baki daya”.
Ta ci gaba da cewa; “gaskiya bani da abin da zance illah in ce Allah ya yi wa ‘ya’yana albarka don sune suke gudanar da wannan hidimar, ga shi kuma Ni ake godemawa don hakan Allah ya kara tsare su a duk inda suke, su kuma jama’a Allah ya baiwa kowa lafiya na gode kwarai da gaske”.
An yi taro lafiya an tashi lafiya.