Daga: Penina Jeje Ali Damaturu
Da yake jawabi ga wadanda suka anfana, Gwamna Mai Mala Buni yace kudaden na wasu tsaruka ne guda biyu na farfaɗowa daga ibtila’in Korona da shirin NG-CARES.
A cewar gwamna Buni tsarukan sun hada da turawa kowanne mutum daga cikin 1,000 Naira dubu dari cikin wadanda ambaliyar ruwan Shekara r 2022 ya shafa, da kuma rarraba Naira dubu goma kowanne wata ga mutane dubu uku da dari biyar da goma 3,510 a fadin jihar.
KARANTA WANNAN: Shugaban APC na Jihar Yobe Yayi Ta’aziya Ga Iyalan Marigayi Abdul Wasiu
A yayin da yake kira ga wadanda suka anfana da suyi anfani da kudin domin bunkasa kansu, Gwamna Buni yace “aika-aikar yan tada kayan baya ya kawo ci baya a harkar tattalin arziki wanda hakan ya jawo talauci a tsakanin al’umma”.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na daukan muhimmancin wadanan taimakon domin bunkasa Rayuwar al’umma, yana da kyau wadanda suka anfana da suyi abinda ya dace domin taimaka wa kansu.
Tun farko data ke jawabi, Komishiniyar jin kai da kawar da ibtila’i ta jihar yobe, Dr. Mairo Ahmed Amshi tace za’a rarraba kudin ne ta tsarin tura kudi na jiha karkashin kulawar Ma’aikatar jin kai domin kawo saukin halin da ake ciki yanzu.
Ta yaba wa gwamnan jihar Yobe domin kawo wa al’umma dauki akan lokaci.
Taron ya samu halartar mataimakin gwmnan jiha Alh. Idi Barde Gubana da sauran manyan ma’aikatu a fadin jihar.
A wani labarin kuma, Najeriya da Cuba Za Su Kara Zurfafa Huldar Abokantaka — Shettima
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana muradin gwamnatin Bola Tinubu na kara zurfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da Jamhuriyar Cuba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga mataimakin shugaban kasar Cuba, Salvador Valdez Mesa, a fadarsa da ke birnin Havana, gabanin taron kolin shugabannin kasashen G77+China da za a fara ranar Juma’a.