Gwamnatin jihar Katsina ta gyara makarantun firamare da sakandare sama da 7,000 a jihar.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa gyaran makarantun na da hadin gwiwa da hukumar kula da ilimin bai daya (UBEC).
Gwamna Aminu Masari ya bayyana haka ne ranar Alhamis din nan a Katsina yayin da yake karbar tsoffin ‘yan majalisar dokokin jihar da suka kai masa ziyarar ban girma.
Ya bayyana cewa an kashe Naira biliyan 30 wajen gyaran makarantu a fadin kananan hukumomin jihar 34.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin jihar ta dauki malamai 5,000 aiki tare da karawa duk malaman da ba su kai shekaru tara ba.
Karanta kuma: Gwamnatin Katsina Ta Haramtawa Malamai Amfani Da Zaurukan WhatsApp
A cewar Masari, wannan wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na inganta harkokin koyo da koyarwa a jihar.
Ya ce yawan daliban firamare ya karu daga miliyan daya zuwa sama da miliyan 2.2 tsakanin shekarar 2015 zuwa bana.
Ya ce hakan ya samu ne saboda dabarun gwamnatinsa a fannin ilimi.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta kuma kashe Naira biliyan 15 wajen gina magudanun ruwa a yankin babban birnin Katsina, domin magance matsalar ambaliyar ruwa.
Ya ce gwamnati na kashe Naira biliyan 4 a duk shekara wajen gudanar da wannan aiki, inda ya ce gwamnati tare da hadin gwiwar bankin duniya sun kuma kashe sama da Naira biliyan 50 wajen magance ambaliyar ruwa da zaizayar kasa.
Gwamnan ya ce an kashe kudaden ne wajen magance ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a kananan hukumomin Katsina, Jibia, Malumfashi da Funtua. (NAN)
A wani labarin kuma: Yajin Aikin ASUU: Dalibin Likitanci A Shekarar Karshe Ya Zama Mai Siyar Da Abinci
Malam Usman Abubakar-Rimi, wanda dalibi ne a shekarar karshe a fannin likitanci da tiyata a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto (UDUS), ya koma mai siyar da abinci a kan titi saboda tsawaitar yajin aikin da malaman jami’ar suke yi.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a ranar Juma’ar nan a Sokoto, Abubakar-Rimi ya ce ya dauki wannan matakin ne domin su samu rayuwa mai inganci yayin da yajin aikin ya tilastawa dalibai barin makaranta.