Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kafa dokar ta baci a duk yankunan da masu aikata laifuka da ‘yan fashin daji ke zaune.
Wannan a cewar Gwamna Tambuwal wanda ya gana da shugaba Buhari a fadar shugaban kasar da yammacin jiya litinin na kimanin mintuna talatin, zai baiwa rundunar soji damar gudanar da ayyukansu ba tare da bari ko kuma cikas ba a dukkan yankunan da sanarwar ta shafa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Gwamna shawara na musamman Muhammed Bello kan harkokin yada labara ya fitar a ranar Litinin.
‘’Wadannan ayyuka, da zarar an yi kuma an shirya aiwatar da su, “ya kamata a yi su lokaci guda a jihohin da ‘yan ta’adda ke da sansani, irin su, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna, Niger da Kebbi; da kuma wasu wurare, inda masu laifin ke da maboya,” in ji sanarwar.
“Gwamna Tambuwal ya kuma yi kira ga shugaban kasar da ya ba da fifiko wajen tura karin dakaru zuwa duk yankunan da ke fama da rikici kamar yadda ya bayar da shawarar sayo nagartattun na’urori, musamman na fasahar zamani wadan da ake amfani da su a yanzu sun ta’allaka ne wajen tura jirage marasa matuka a duniya.
“Saboda yanayin tsaro a yankin Sahel, wanda ya kara ta’azzara rikici a yankin, akwai bukatar a nemi kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS da ta nemi hadin kai da Birtaniya da Faransa da kuma Amurka.”
Dimokuradiyya ta rawaito Sanarwar tana kuma yin kira ga shugaban kasar, da ya yi la’akari da ra’ayoyin jama’a da ke nuni da kiran jami’an da suka yi ritaya domin shiga yakin da ake da ‘yan ta’adda da kuma daukar karin jami’ai a dukkanin bangarorin jami’an tsaro.