Gwamnonin jihohin Yobe da Kogi, Mai Mala Buni da Yahaya Bello sun mika ta’aziyyar su ga abokin aikinsu Abdullahi Sule bisa rasuwar dansa Hassan Sule.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Buni, Mamman Mohammed, ya fitar ta ce gwamnonin sun je Gudi, gidan gwamnan jihar ne domin jajanta masa da jama’arsa bisa rasuwar dansa Hassan mai shekaru 36 da haihuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Dan Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Rasu
Sun yi addu’ar Allah Ta’ala ya gafarta wa marigayin, ya kuma ba shi hutu na dindindin.
Buni da Bello a cikin sanarwar sun kuma yi addu’ar Allah ya baiwa Gwamna Sule da iyalansa da al’ummar Jihar Nasarawa hakurin jure wannan babban rashi.
Mai martaba Sarkin Lafia, Sidi Bage Muhammad, wanda ya yi magana a madadin iyalai da al’ummar Jihar Nasarawa, ya gode wa gwamnonin biyu da suka bayyana dan’uwansu da abokin aikinsu a wannan lokaci.
Hassan Sule ya rasu ne a ranar Alhamis din da ta gabata kuma an yi jana’izarsa a garin Gudi da ke jihar Nasarawa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A wani labarin kuma, Kanin Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar NNPP, ‘Yan Uwansa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP
Kanin Haliru Jika, dan takarar gwamna na jam’iyyar, NNPP, a jihar Bauchi, Buhari Jika, da wasu ‘yan uwansa sun fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP.
Wadanda suka sauya sheka suna goyon bayan takarar Gwamna Bala Mohammed ne a karo na biyu.