Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya yi rashin dansa na farko, Daily Post ta rawaito.
Hassan Sule, mai shekaru 36, ya rasu ne a yammacin ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Tsaurara Matakan Tsaro Yayin Da Kotu Ke Yanke Hukuncin Zaben Gwamnan Osun
Marigayin wanda ya auri matarsa a watan Yunin bara, ya rasu ne a garin Lafia babban birnin jihar.
Babban sakataren yada labaran gwamnan, Ibrahim Adra, ya tabbatar da rasuwar.
Sanarwar da kakakin ya fitar a ranar Juma’a ta lura cewa mutuwar ta kasance “kwatsam”.
Za a yi jana’izar Hassan a garin Gudi da ke karamar hukumar Akwanga a safiyar yau kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A wani labarin kuma, Tabbas Tarihi Ba Zai Manta Da Gudunmawar Dana Baiwa Najeriya Ba – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana amannarsa wajen cewa tarihi zai musu adalci domin sanya su cikin wadanda zai dinga tunawa da su, musamman idan aka yi duba dangane da tarihin yadda suka gaji kasar.
Shugaba Buhari a cewarsa wata sanarwa da mai Magana da yawun sa Femi adesina ya fitar, jamiyyar APC ta samu mulkin kasar nan a lokacin da take cikin yanayi na fama da matsalar tsaro da kuma tabarbarewar tattalin arziki.