Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Mai Mala Buni ya taya al’ummar Yobe murnar cika shekaru 31 da kafuwar jihar.
Buni a cikin wata sanarwa ta hannun babban daraktan yada labaran sa da hulda da manema labarai, Alhaji Mamman Mohammed ranar Asabar a Damaturu, ya yabawa magabatansa bisa gudunmawar da suka bayar wajen dora jihar a kan turbar zaman lafiya da ci gaba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Gargadi Masu Amfani Da Kakinta A Shafukan Sada Zumunta
Gwamnan ya ce, kowanne daga cikin shugabannin da suka shude ya bayar da gudunmawa sosai wajen ganin jihar ta kasance a yau, yayin da jama’a suka ba da goyon baya da hadin kai.
“A matsayinku na shugabannin jihar a lokuta daban-daban, kun ba da gagarumar gudunmawa ga jihar wanda ya ba mu dukkan alfahari,” in ji shi.
Ya kuma yabawa al’ummar jihar nan na gida da waje, bisa goyon baya da gudunmawar da suke bayarwa ga gwamnatocin da suka shude.
“Ina yaba muku musamman kan juriya da goyon baya da hadin kai wajen gina jiharmu abar kauna.”
“Karfin halin ku ya sa wannan gwamnati ta samu ci gaba cikin sauri da kuma farfado da jihar bayan rikicin Boko Haram na tsawon shekaru goma,” in ji shi.
Buni ya yi godiya ga Allah madaukakin sarki bisa zaman lafiya da ake samu a fadin jihar, inda ya bukaci jama’a da su ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya da samun kwanciyar hankali.
Ya ce tallafin da aka bai wa gwamnatinsa ya baiwa gwamnati damar sake gina makarantu, samar da karin cibiyoyin kiwon lafiya, gidaje, gina tituna da kuma kammala filin jirgin saman dakon kaya da dai sauransu.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da ayyuka da tsare-tsare na jama’a domin inganta rayuwar al’umma.
Buni ya yi addu’ar Allah ya karo shekaru masu yawa da samun ingantacciyar zaman lafiya da tsaro da wadata da kuma ci gaban jihar cikin gaggawa.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, marigayi shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha ne ya kirkiro Jihar Yobe a ranar 27 ga watan Agustan shekarar 1991.
A wani labarin kuma Gwamnatin Buhari Ta Tallafawa Wata Jiha Da Kayan Abinci
Gwamnatin tarayya a ranar Asabar ta raba buhunan abinci iri-iri 8,028 ga marasa galihu a jihar Gombe.
An mika kayayyakin ne ga kungiyoyi da ba su wuce 50 ba, da suka kunshi cibiyoyin gargajiya da na addini, wadanda ake sa ran zasu rabawa talakawan dake mazabarsu