Gwamna Douye Diri, na jihar Bayelsa ya yi afuwa ga fursunoni tara na Cibiyar Kula da Gyaran Hali ta Nigeria dake Okaka, a Garin Yenagoa babban birnin jihar.
Diri wanda ya ba da sanarwar karimcin lokacin da ya ziyarci cibiyar a jiya Talata, ya ce, ya yi hakan ne bisa shawarwarin da Kwamitin Kula da Afuwa ga Mamu laifi ya bayar.
Fursunonin da aka yafe sun hada da: Tombra Tiemo , Sunny Okpara , Timi Okpo, Ebikabowei Mokina da Joy Nekekpeme.
Sauran sune Joy Victor , Jacob Anthony Jacob, Power Ekparaolaokumo da Mutecliff Tobi Olori.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC ta nuna damuwa kan Matsalar Tsaro a Anambra
Gwamnan ya shawarci fursunonin da aka yi wa afuwa da su canza halayensu su zama wakilai nagari cikin al’umma.
Ya nuna rashin jin dadinsa kan adadin fursunonin da ake tsare da su, inda ya kara da cewa, hanya daya tilo da za a rage yawan mutane a cibiyar ita ce,rage laifuka a jihar.