By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2022 na naira biliyan 278.58bn.
Taron ya samu halartan shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna Yusuf Zailani da sauran manyan jami’an majalisar da kwamishinoni da mataimakan gwamnan.
Gwamnan ya bayyana cewa majalisar ta kara yawan kasafin daga naira biliyan 233 da bangaren zartarwa ya gabatar zuwa naira biliyan 278.58bn domin karbar karin bukatun ayyukan.
Kwamishinan kasafi da tsare-tsare, Muhammad Sani Abdullahi, yace kasafin da aka rattabawa hannu ya kunshi jarin naira biliyan 184.53 da kuma naira 94.05bn wanda za a sake kashewa akan rashi kashi 66:37.
Bangaren ilimi wanda ya samu (Nira biliyan 41.66), sai bangaren lafiya wanda ya samu (Naira 28.63bn) da kuma bangaren ci gaban zamantakewa wanda aka ware masa (Naira biliyan 19.37), da kuma Naira biliyan 28.94 na bangaren zuba jari da aka ware domin ayyukan gwamnati da ababen more rayuwa da kuma Naira 8.79bn na gidaje da raya birane.
Sannan ya kara da cewa jihar na shirin naira biliyan 150bn a matsayin kudaden shiga na cikin gida na shekara (IGR) da kuma kudaden shiga na cikin gida na Naira 50bn.