• Kungiyar Makafi na Arewacin kasar nan Taga dacewar gwamnan Kuma ta bashi wannan lambar yabon.
• Gwamna Ganduje ya lashe wanan kyautar ne lokacin da kungiyar ta gudanar da Taron ta na shekara shekara a Kano.
• A nashi bangaren Gwamna Ganduje ya yabawa kungiyar bisa goyan baya da suka bashi wajan Hana bara a fadin jihar Kano.
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya halarci rufe taron kungiyar makafi na Arewa, wato (AREWA FREEDOM OF THE BLIND), wanda suke gudanar wa shekara shekara.
Taron nasu na wannan shekarar sun gudanar dashi ne, a harabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, inda su ka gudanar da addu’oi, wasanni, da kade-kade irin nasu na makafi.
Kungiyar ta karrama Mai Girma Gwamna da lambar yabo da kuma bashi sarautar “Jagoran zaman lafiya na arewa”, yayin da suka shaida wa jama’a cewa, Gwamnan shine Gwamnan da yafi son zaman lafiya, da kula da masu bukata ta musamman.
A jawabin sa, Gwamnan ya yabawa Shugabancin kungiyar, bisa ga yadda suka goyi bayan kudirin gwamnati, na hana bara a fadin jihar kano, inda ya tabbatar musu da cewa, gwamnatin sa zata cigaba horar da makafin da basu jari, domin su cigaba da dogara da kan su, da kuma daukar nauyin karatun yayan su.
KARANTA WANNAN LABARIN : Magatakaddar Jam’iyar APGA ta kasa ya koma APC a Zamfara
Yayin taron Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana tare da sakataren Gwamnati Alhaji Usman Alhaji, Daraktan yakin neman zabe, Dattijo Alhaji Nasiru Aliko Koki, Kwamishinan ayyuka na musamman Hon. Mukhtar Ishaq Yakasai,
Inda sauran suka hadar da: Kwamishininan yada labarai Kwamared Muhammad Garba, da mai bai wa Gwamna shawara akan kungiyoyi masu zaman kan su, Hajiya. Yardada Maikano, da kuma Shugaban Hukumar bada agajin gaggawa, Honarabul Sale jili da sauran jami’an gwamnatin jihar Kano
Comments 2