Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kori Engr. Mu’azu Magaji Wanda aka Fi Sani da Dansarauniya, a matsayin Babban Shugaban Kwamitin Man Fetur na NNPC/AKK da Kwamitin kula da aikin Iskar Gas.
Wannan shi ne karo na biyu da gwamnan zai sauke Magaji daga Mukamin sa, bayan sallamar sa na farko a matsayin kwamishina, bayan wani rubutu da ya yi a Facebook, Wanda rubutu ya nuna cewa, izgili ne ga mutuwar Abba Kyari, tsohon shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu sakamakon cutar COVID-19.
A sabon korar sa da aka yi, A cewar Gwamnan, ta hannun sanarwar Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Muhammad Garba, ya zargi Magaji da rashin kyakkyawan aiki da kuma rashin cika alkawari.
An nada Magaji ya jagoranci kwamitin ne tun a watan Afrilu shekarar 2020, don sa ido kan yadda ake aiwatar da aikin gas na AKK
KARANTA WANNAN LA ARIN: Lalong ya Rantsar da Sabbin Shuwagabannin Kannann Hukumomi a Filato
Amma sanarwar ta ce, tsohon kwamishinan da ake takaddama a kansa ya kasa aiwatar da kuma sauke nauyin da aka dora masa na kula da aikin.
A cewar sanarwar, jagorancin kwamitin, wanda ya hada da wasu abubuwa, tare da hadin gwiwa da NNPC kan aiwatar da aikin kan lokaci, bai kasance cikin aiki ba, don cimma burin da ake so.
Sanarwar ta ce, gwamnan ya umarci Magaji da ya mika lamuran kwamitin ga mataimakin shugaban zartarwa, Aminu Babba Dan’Agundi, da kuma Sarkin Dawaki Babba.
Comments 1