By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi DSP Abdulkadir Rano, jami’in dan sanda reshen Jibia a jihar Katsina da kuma masarautar Rano bisa rasuwarsa.
Wasu ‘yan bindiga sun kashe Rano a lokacin da yake bakin aiki a jihar Katsina.
Sakon na gwamnan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Abba Anwar, babban sakataren yada labarai na Ganduje ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Bayanin mutuwarsa na da ban tausayi. Kuma ya rasu ne a lokacin da Najeriya ta fi bukatarsa. Ya kasance daya daga cikin manyan jami’an da ke aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya.
“Hakika mun yi rashin wani jami’i mai kishin kasa wanda yanayinsa na kishin kasa ya kara kima ga hidimar da ya bari. Karfinsa da jajircewarsa na yin aiki sun yi fice kuma abin yabawa ne.”
Ganduje ya bayyana Rano a matsayin daya daga cikin mafi kyawun jami’an ‘yan sanda, wanda ba a iya auna kokarinsa na ceto rayuka da dukiyoyi.
Yayin da yake jajantawa iyalan marigayi DPO, gwamnan ya ce Najeriya ta yi rashin dan sanda mai gaskiya.
“A madadin gwamnati da jama’ar jihar Kano, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalansa da rundunar ‘yan sandan Najeriya da kuma masarautar Rano. Allah ya gafarta masa dukkan kurakurensa, ya kuma saka masa da ayyukansa na alheri,” inji shi.