By Ishaq Dabai
Kamar yadda ya umarci dukkan kwamishinoni, da masu bada shawara da su halarci faretin ranar samun ‘yancin kai
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yace Kwanaki kadan yarage ga Majalisar Jam’iyyar APC mai mulki a jihar inda ta shirya tsaf don babban taron jihar da za a gudanar a ranar 16 ga watan Oktoba.”
Ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar zartarwa na jihar, kafin fara shi, wanda aka gudanar a Africa House,dake gidan Gwamnati Kano a ranar Talata.
Yace,”An gudanar da mazabu na unguwanni. Hakan ya biyo bayan manyan majalisun kananan hukumomi, bayan rantsar da shugabannin jam’iyyar na mazabu, yanzu muna jiran rantsar da shugabannin kananan hukumomin da aka zaba ‘yan makonni baya,” in ji shi.
“Muna shirye shiryen babban taron jiha. Muna yin dukkan shirye shiryen da suka dace don gudanar da babban taron majalisar jihar,” in ji shi.
A halin da ake ciki, ya umarci dukkan kwamishinoni da duk masu ba da shawara da su halarci faretin ranar samun ‘yancin kai da za a fara ranar Juma’a, 1 ga Oktoba.
“Kwamishinan Yada Labarai na jihar Malam Muhammad Garba shine wanda zai jagoranci bikin ranar samun‘ yancin kai.
Kazalika ya kara da cewa yana kuma umartar dukkan kwamishinoni da masu bada shawara da su kasance a wurin ranar Juma’a, yayin faretin ranar ‘yancin kai, ”in ji shi.