By Abbas Yakubu Yaura
‘Yan sa’o’i kadan bayan furucinsa na cewa mulki zai koma ko dai Ukwa axis ta Abia ta kudu ko Abia Arewa, an tsige tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Adolphus Wabara, daga matsayin shugaban majalisar gudanarwa na jami’ar jihar Abia, Uturu.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Rivers Ta Rage Matsayin Shugabannin Makarantu 14, Ta Soke Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu 21
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Abia Barista Chris Ezem, gwamnan jihar, Okezie Victor Ikpeazu, da maziyartan jami’ar jihar Abia, Uturu, sun amince da rusa majalisar gudanarwar jami’ar nan take.
Nan take gwamnan ya amince da sake fasalin majalisar gudanarwar kamar haka; Cif Mba Okoronkwo Ukariwo – Shugaban, Cif Obinna Njoku – memba, Sanata Emma Nwaka – memba, Cif Chinwe Nwangang – memba.
Sauran sun hadar da Cif Ndukwe U Ndukwe – mamba, da Dakta Jonas Ibeaja – mamba, Barista C Nwokeukwu (SAN) – memba da kuma Babban Sakatare, Ma’aikatar Ilimi – memba.
Tun da farko Wabara, wanda shi ne Sakataren Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP, ya gargadi gwamnatin Jihar da jam’iyyar cewa za su yi asarar Abia idan wani Ngwa ya yi yunkurin maye gurbin Ikpeazu.
Wabara ya yi gargadin cewa duk wani yunƙuri na ganin wani ɗan Ngwa ya gaji Ikpeazu wanda shi ma ɗan Ngwa ne ba zai yi tasiri ga PDP ba.
Inda ya kara da cewa yayin da jam’iyyar za ta iya samun ƙuri’ar zanga-zanga a Abia, a babban zaben mai zuwa 2023.