PDP a Cross River na Murna akan Korar Ƴan Majalisu 20 — Cewar Ikem
Jam’iyyar PDP ta yabawa Babbar Kotu data kori ƴan Majalisu 20 da suka canja Jam’iyyar zuwa wata a ƴan kwanakin da suka gabata.
Shugaban Jam’iyyar PDP na Jahar Mr Venatius Ikem a ranar Talata yace Mambobin Jam’iyyar na matuƙar jindaɗi akan hukuncin daya kori ƴan majalisun da suka koma Jam’iyyar APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Rivers Ta Rage Matsayin Shugabannin Makarantu 14, Ta Soke Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu 21
A yanke hukuncin da Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya yanke a ranar 21 ga watan Maris, Kotun tace akwai buƙatar subar kujerun su, tunda suka ƙyale Jam’iyyar data yi sanadin kawo su a kujerar.
Hukuncin ya biyo bayan wata ƙara da Jam’iyyar PDP ta shigar mai Lamba ta FHC/ABJ/CS/975/2021.
Shugaban Jam’iyyar yace suna cikin murna marar misaltuwa akan nasarar da jam’iyyar su ta samu.
A ɓangaren shi Mr Mike Ojisi, Sakataren Yaɗa Labaru na Jam’iyyar PDP yace a shirye suke su sanya ƴan takarar su ga guraben ƴan majalisar, inda ya ƙara dacewa hukuncin Kotu abun ayaba ne.