By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kungiyar malamai ta Najeriya reshen jihar Neja, Mohammed Akayago, ya umurci malaman makarantun firamare a jihar dasu fara yajin aiki na zaman gida idan har an biya su wani kaso daga albashin watan Disamba.
Akayago ya bayar da umarnin ne a Minna ranar Litinin yayin da yake jawabi ga manema labarai kan sakamakon taron kungiyar da suka gudanar.
Ya bayyana cewa malaman firamare a jihar ba zasu dinga karbar albashi bisa wani kaso ba, wanda yace ya saba wa dokar kwadago.
“Babu wani magana a cikin dokar kwadago da tace ya kamata gwamnati ta rika biyan albashi kan bisa wani kaso a kowane mataki saboda matsalar tattalin arziki ba,” inji shi.
Shugaban ya bayyana cewa tun watanni 5 da suka gabata malaman makarantun firamare a jihar suna karbar wani kaso na albashin su, wanda yace hakan ya yi musu illa, wanda hakan kuma yasa suke fuskantar wahalar biyan bukatun iyalansu.
“Gwamnatin jihar a cikin watanni biyar da suka gabata tana biyan malaman makarantun firamare a cikin bisa wani kaso daga albashin su kuma hakan ya jawo musu wahala dasu da iyalansu,” in ji Akayago.
Ya kara da cewa idan har a karshen watan nan babu wani martani mai kyau daga gwamnatin jihar, malaman firamare basu da wani zabi illa zama a gida har sai an biya musu bukatunsu.