A safiyar ranar Laraba ne gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya gabatar da cekin kuɗi na naira miliyan 20 ga iyalan Marigayi Kanal Dahiru Chiroma Bako, kwamandan sojin da ya mutu sakamakon harin mayaƙan Boko Haram a Damboa.
A yayin da Zulum yake halartar jana’izar babban sojan a ranar Talata, 22 ga watan Satumba, ya yi alƙawarin bai wa iyalan mamacin kyautar Naira miliyan 20 domin su ci gaba ɗaukar nauyin rayuwarsu.
Gwamnan ya kuma ya sanar da cewa za a gina wa marayu da matar mamacin wadataccen gida duk inda suke so a faɗin Najeriya domin su ci gaba da rayuwarsu a ciki.
“Na samu labarin cewa akwai sojoji uku da su ma suka rasa rayukansu tare da Kanal Bako, saboda haka, na ba da gudunmuwar kuɗi na naira miliyan biyu ga iyalan kowanne daga cikinsu”, cewar Zulum.
Yayin da take karɓar takardar cekin kuɗin, matar marigayi Kanal Bako, Rukayya Dahiru, ta yi godiya ga gwamnatin a bisa karamcin da ya yi musu.
Wannan ba shi ne karo na farko da mayaƙan Boko Haram ɗin ke kashe sojin ƙasar nan ba.
Sai dai daga ɓangarensa Zulum ya yi hakan ne domin kyautata rayuwar iyalan marigayin tare da basu ƙwarin guiwar yin ingantacciyar rayuwa.