Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu ya rage karfin ikon wasu sarakuna ta hanyar daukaka wasu Obas zuwa manyan sarakunan gargajiya.
Gwamnan wanda ya hana rufe kasuwanni saboda bukukuwan gargajiyar ba tare da amincewar sa ba, ya kuma daukaka wasu sarakuna zuwa matsayin Obas a cikin al’ummar jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: Wasu Ma’aikata Sun Makale Yayin Da Wani Ginin Beni Ya Ruguje A Abuja
Ya ce babu wasu shaguna a wuraren zaman jama’a da za a rufe idan aka ba da izinin rufe kasuwannin ba.
Sarakunan, wadanda aka daga darajarsu daga sarakunan gargajiya na B zuwa mataki A sune Owa-Ale na Iyometa, Ikare, karamar hukumar Akoko ta arewa maso gabas; Ajana of Afa Okeagbe, Akoko ta arewa maso yamma; Alale of Akungba, Akoko ta kudu maso yamma.
Wadanda aka daukaka a Akure ta arewa, Akure ta Kudu da Ifedore sune Okiti na Iju, Ogbolu na Ita-ogbolu, Oloba na Oba-Ile, Alara na Ilara mokin, Olujare na Ijare, Olowa na Igbara-Oke.
A Ondo ta Kudu, kujerar gargajiya da ta tashi sune Oluoke na Okeigbo, Maporure na Agerige, Eletikan na Etikan, Ahaba na Ajagba, Odogbo na Omiland, Larogbo na Akotogbo, Orunja na Odigbo, Halu na Ode-Aye, Orungberuwa na Erinje.
Sauran sun hada da Ojomo-Luda na Ijebu-Owo, Olupele na Ipele, Elemure na Emure-Ile, Olumoru na Imoru da Olute na Ute.
Kwamishiniyar yada labarai da wayar da kan jama’a Mrs Bamidele Ademola-Olateju, ita ce wacce ta yi magana bayan taron majalisar zartarwa na jihar na mako-mako, ta ce an warware wasu rikice-rikice a wasu al’ummomi tare da daidaita wuraren da ake cece-kuce.
Ta ce har yanzu batun ‘Premounted’ yana nan yana jiran a gyara dokar masarautar jihar.
Olateju ta ce: “Wasu mutane sun yi kama da Olofun na Irele a karamar hukumar Irele da Olu na Igodanlisa a karamar hukumar Okitipupa ba tare da amincewar majalisar zartarwa ta jihar ba.”
“Irin wadannan mutane za a kama su kuma a bincike su kan laifin da suka yi a kan dokar sarautar jihar.”
“Har ila yau, mataimaka na jihar ta lura da izinin da aka bayar don gudanar da bukukuwan gargajiya. A nan gwamnati ta sake nanata cewa ba za a rufe kasuwanni ba sai da izinin gwamna.”
“Idan aka ba da izini, irin wannan amincewar za ta iyakance ne ga kasuwar Oba kawai, ba shaguna a wuraren zaman jama’a ba.”
Babban Lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a Sir Charles Titiloye ya ce Gwamna Akeredolu a shirye yake ya aiwatar da rahoton kwamitin mai shari’a Ajama don duba batutuwan da suka shafi sarauta a jihar, wanda aka gabatar shekaru takwas da suka gabata.
Ya bukaci wadanda aka yiwa obas da hakimai da su jira Farar Takarda na gwamnati a kan karin girman su.
A wani labarin kuma Lauyan Dake Kare Hakkin Dan Adam Inibehe Effiong Ya Shaki Iskar ‘Yanci Daga Gidan Yari
Inibehe Effiong, lauya mai fafutukar kare hakkin bil’adama, ya sake samun ‘yancinsa bayan ya shafe wata guda a gidan yari a Uyo, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
An ga Mista Effiong a cikin wani faifan bidiyo kai tsaye yana fita daga gidan yari ga hannun abokan aikinsa wadanda suka taru a kusa da Wellington Bassey Way, Uyo, da karfe 8:00 na safe.