Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a ranar Litinin ya rantsar da Kwamishinoninsa guda 23, inda ya yi kira gare su da su yi aiki tukuru wajen cimma kyakkyawan narasa a ma’aikatar da aka damka musu.
Lalong ya ce zai taimaka musu domin ganin sun cimma nasara a ayyukan da aka damka musu, sai dai ya ce ba zai yadda da son jiki da rashin son yin aiki ba.
Gwamnan ya nemi hadin kan Kwamishinonin, tare da aiki tukuru wajen cimma nasarar gwamnatinsa.
Dan jarida Dan Manjang, kuma tsohon Kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar, an maishe a matsayin sabon Kwamishinan sadarwa da yada labarai, inda shi kuma Yakubu Dati, ya koma Kwamishinan Filaye .
Sauran sun hada da; Pam Bot Mang, a matsayin Kwamishinan ayyuka, sai kuma Victor Lapang, Kwamishinan wasanni da ci gaban matasa, sai kuma Elizabeth Wapmuk, a matsayin Kwamishinar Ilimi a matakin Sakandare,sai Sylvanus Tapgun, Kwamishinan kananan hukumomi da lura da ayyukan Masarautu.
Har wala yau sauran da aka ratsar su hada da; Bitrus Zulfa, Kwamishia gidaje, Ibrahim Bello, Kwamishinan ruwa da makamashi, sai Chrisantus Ahmadu, Babban Jojin Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a. Sai kuma Dr Nimkong Ndam, Kwamishinan lafiya, sai kuma Alhaji Dayyabu Garga, Kwamishinan tsare-tsare da ci gaban birane.
Dr Istifanus Finangwai ya zama Kwamishinan noma da kiwo, sai Tamakat Weli, Kwamishinan al’adu da kuma yawon bude da ido da walwala, inda kuma shi kuma Dr Regina Soemlat, aka ba rantsar da shi a matsayin Kwamishinan kudi, sai kuma Kakmena Audu, Kwamishinan ilimi mai lura da makarantun gaba da Sakandare, sai kuma Usman Idi, Kwamishinan muhalli.
Jude Dakur a matsayin Kwamishinan ci gaban ma’adanai shi kuma Sylvester Wallangko, a matsayin Kwamishinan kasafin kudi da tattalin arziki, inda shi kuma Dung Gyang, a matsayin Kwamishinan kimiyya da fasaha, sai kuma Jerry Werr, Kwamishinan ayyuka na musamman da ayyukan gwamnati.
Sai kuma Alhaji Muhammad Abubakar, Kwamishinan sufuri, a yayin da aka biwa Rebecca Sambo Kwamishiniyar lura da ayyukan mata.