Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe ya rantsar da Kwamishinoninsa 21 tare da masu ba shi shawara mutum 15 a matsayin membobin kwamitin zartaswa na jihar, inda ya bukace su da su tabbata sun rike amanar al’umma da aka damka musu a hannunsu ta hanyar ba su wadannan mukamai.
Gwamnan ya ce ya kaddamar da sabbin masu taimaka masa ne a Gombe domin ganin gwamnatinsa ta yi ayyukan a zo a gani a jihar. Gwamnan ya rantsar da Kwamishinoninsa din ne da masu ba shi shawara a jiya Asabar.
A cewarsa, yanzu al’umma sun zuba ido domin ganin sun yi musu aikin da aka zabe su su yi. Inda ya ce yanzu abin da ya rage wa gwamnatinsa shi ne su yi aiki tare domin ganin sun gudanar da kyakkayawan shugabanci domin ganin al’umma ta sharbi romon dimukuradiyya a jihar Gombe.
A madadin sabbin wadanda aka rantsar din, Zubairu Umar, Kwamishinan Shari’a kuma Babban Jojin jihar, ya godewa gwamnan, tare da yi masa alkawarin cika wa gwmanan manufofinsa da fatansa domin amfanar al’umma Gombe