Hukumar ba da tsaro ta NSCDC reshen jihar Anambra ta cafke mutum 35 ciki harda wata mata mai suna Nkeoma Ezuma, bisa zarginsu da safarar mutane.
David Bille, Kwamandan NSCDC din a jihar, shi ne ya bayyanawa kafafen watsa labarai hakan a yau Asabar a garin Awka.
Billie ya ce Ezuma, wanda ita ce mai gidan abincin dake Agulu Ezechukwu Community a karamar hukumar Aguata a jihar, an kama ta ne a ranar 5 ga watan Nuwamba a Agulu Ezechukwu, a yayin da take shirye-shiryen safarar wadansu zuwa kasashen waje.
Ya ce a binciken da suka fara yi, ya nuna wacce ake zargi ta kware a harkar safarar mutane musamman kananan ‘yan mata da ba su wuce shekara 17 zuwa 25 ba, inda take kai su kasar Mali da wadansu kasashen Afrika domin yin karuwanci.
Hukumar ta ce ta ceci mutane uku da suka hada da;- Ifeoma Ezenwanne, 17, Chidimma Charles, 18 da kuma Mmesoma Onwue, 17 wanda aka tsara za a kai su kasar Mali domin yin ayyukan karuwanci.
Billie ya ce hukumar ta su sun samu bayanan sirri ne akan ayyukanta, da gurbatacciyar kasuwancin safarar mutanen da take yi, inda daga nan ne suka sanya mata ido, kafin daga bisani suka kamata a ranar 5 ga watan Nuwamba.
Ya ce wacce ake zargi ta tabbatar da zargin da ake mata, kuma za su mika ta zuwa ga hukumar haramta safarar mutane ta kasa wato NAPTIP da zarar sun kammala bincike..
Har wala yau hukumar ta ce ta kuma kama wani mutum mai suna Emeka Eyiuche, dan shekara 43 wanda ya damfari mutane da suka kai goma da sunan zai nema musu aiki.
A cewarsa, Eyiuche ya taso ne a Umudisi Abacha a karamar hukumar Idemili North, kuma ya kware wajen ayyukan damfarar al’umma da sunan zai samo musu aiki.
“A ranar 7 ga watan Nuwamba, 2019 da misalin karfe, 12:00 hukumar ta cafke Emeka Eyiuche. Wanda ake zargi ya damfari wadansu da suka kai mutum 10 naira dubu 204, da sunan zai sama musu aikin yi da hukumar NSCDC.” In ji hukumar.
Billie ya ce a halin yanzu yana hukumar NSCDC a garin Awka wanda yana taimaka musu wajen wadansu binciken a cewar hukumar.