- Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya jajantawa takwaransa na jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani da Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, dangane da rugujewar masallaci
- Gwamnan ya bayyana matukar alhininsa game da asarar rayukan da aka yi, sanadiyyar ruftawar ginin masallacin
- Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da kuma baiwa wadanda suka samu raunuka sauki cikin gaggawa
Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris, ya jajantawa takwaransa na jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani da Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, dangane da rugujewar masallacin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai mai dauke da ratta ba hannun babban sakataren yada labaran gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Idris wanda ya fitar a Birnin Kebbi a yammacin Lahadi.
KARANTA WANNAN: Hedikwatar Tsaro Ta Musanta Karbar Bukatar Juyin Mulki
Gwamnan ya bayyana lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 12 a matsayin wani abin takaici da kuma babban rashi ba ga Masarautar Zariya da Zazzau kadai ba har ma da jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya.
Idris ya bayyana matukar alhininsa game da asarar rayuka da aka yi, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a lamarin.
Idris ya bukaci Masarautar da daukacin al’ummar Jihar Kaduna da su amince da yardar Allah Ta’ala cikin aminci, ya kuma yi addu’ar Allah SWT ya karbi shahadarsu ya kuma ba su aljannatul Firdaus.
Da yake jajantawa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu, gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da kuma baiwa wadanda suka samu raunuka sauki cikin gaggawa.
Kazalika ya yi addu’ar Allah ya kawo karshen wannan mummunar dabi’a da kada ta sake faruwa.
A wani labarin kuma, Kano: NEMA Ta Raba Kayan Agaji Ga Mutane 22,658 Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
Hukumar NEMA a kokarinta na rage wahalhalun da bala’in ambaliyar ruwa ya shaifar, hukumar ta fara rabon kayan agaji ga magidanta 22,658 a Kano
An shawarci wadanda suka ci gajiyar kayayyakin da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata domin inganta zamantakewa da tattalin arzikinsu da kuma kaucewa sayar da su
Kananan hukumomi 22 da ke shiyyar sanatoci uku da ke jihar ne za su ci gajiyar kayayyakin tallafin
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA a kokarinta na rage wahalhalun da bala’in ambaliyar ruwa ya shaifar, hukumar ta fara rabon kayan agaji ga magidanta 22,658 da bala’in ambaliyar ruwa ta shekarar 2022 ya shafa kuma masu rauni a Kano.
Darakta Janar na NEMA, Mista Mustapha Ahmed-Habib ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da rabon kayan tallafin ga wadanda suka ci gajiyar tallafin a Kano.