Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq da Sarkin Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar sun halarci Jana’izar Marigayi Mai Martaba sarkin Lafiagi Alhaji Sa’adu Kawu Haliru da ya guda na a jiya juma’a.
Mariya Haliru ya rasu ne a ranar Alhamis din da ta gabata, a wani babban asibitin kasa dake babban birnin tarayya Abuja, Kuma ya rasu ya na da shekara 86 a duniya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fussunoni Hudu sun guda a cibiyar Gyaran hali dake Jos
Gwamna AbdlRazaq ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin sa, da shuka hada da: Shugaban majalissar dokokin jihar Injiniya Yakubu Danladi-Salihu, da Mambobin majalissa, Sakataran Gwamnatin jihar Farfesa Mamman Saba Jubril, Kwamishinan kananan hukumomin da cigaban unguwani, Akitec Saifudeen Muhammad, da kuma Mukaddashin shugaban jami’iyar APC a jihar Alhaji Abdullahi Samari.
Kazalika Jana’Izar ta sami halartan wasu manyan Sarakunan Gargajiya da su ka hadar da: Wakilin Mai Martaba Sarkin Ilorin Alhaji Aliyu da Balogu Gambari wato Sarkin Etsu Patigi, Alhaji Ibrahim Umar Bologi II, Sarkin Kaiama Alhaji Muazu Omar, Sarkin Etsu Tsaragi Alhaji Aliyu NdaKpoto, Sarkin Shonga Dakta Haliru Yahaya.
Sauran sun hada da Sarkin Olupako Oba Haruna Olawale, da Babban Limamin Gambari Alhaji Sulaiman AbdulAzeez. Da kuma wasu manyan mutane daban-daban.
Comments 1