Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya ce dole ne gwamnati ta yi iya kokarin ta don horar da likitoci ‘yan asalin Jihar don dakile matsalar daukewar kafa da sunan yajin aiki da wasu likitocin waje suke yi ba tare da sun fahimci kalubalen da ke addabar jihar ba.
Injiniya Sule ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar daliban Jami’ar Jihar Nasarawa Keffi (NSUK), wadanda suka kawo ziyarar girmamawa a gidan Gwamnati, ranar Talata.
Cikin Jawabinsa Gwamnan ya yi watsi da babban matakin rashin kulawar da wasu likitocin a jihar suka nuna, wadanda hakan da suka yi ya karfafa gwiwa kan matsalolin kiwon lafiya da tattalin arziki da kuma cutar COVID-19.
Injiniya Sule ya bayyana bacin ransa cikin “raɗaɗi” na halin da likitocin da ke aiki a asibitoci suka zaɓi su ci gaba da kasancewa a zaune ba tare da aiki ba a lokacin da cutar nan take kashe mutanen duniya, sun bar mutanen jihar na fama da matsananciyar wahala.
Yayin da yake yaba wa gwamnan farko na jihar, Sanata Abdullahi Adamu saboda kirkirar jihar, Gwamna ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin cewa sabuwar Kwalejin lafiya ta kafu a Jihar daram.