Fulani makiyaya a jihar Ondo sun ce sanarwar da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu ya yi na cewa ya ba su kwanaki bakwai su bar dazukan jihar ya zo masu da mamaki.
Sarkin Fulani na jihar Alhaji Ali Dogo ya ce sanarwar ta zo masu da mamaki ne saboda sun cimma matsaya da gwamnan jihar a baya.
“Ban ji daɗi ba saboda mu ƙungiyar Fulani makiyaya mun je har gaban gwamna, aka ce mu haɗa kai da gwamnan zai ba mu kayan aiki mu yi maganin duk wani mugu.
“Idan bafulatani ya yi ɓarna mun yarda a kama shi dole ya biya ɓarnar da ya yi. Amma bafulatani na daji da shanun shi sai a ce ya yi garkuwa da mutane, ya yi sata. Duka wannan ba gaskiya ba ne,” a cewar Alhaji Ali Dogo.
Gwamna Akeredolu ya bai wa makiyaya wannan wa’adi ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin inda ya ce su ne sanadin galibin sace-sacen mutanen da ke faruwa a jihar tasa.
Gwamna Akeredolu ya bai wa makiyaya wannan wa’adi ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin inda ya ce su ne sanadin galibin sace-sacen mutanen da ke faruwa a jihar tasa.
A cewarsa, sun dauki matakin ne da zummar tabbatar da tsaron rayuka da na kaddarori a jihar ta Ondo yana mai bayar da umarni ga jami’an tsaro su tabbatar da an aiwatar da dukkan umarnin da ya bayar.
Gargadin da gwamnan jihar Ondo ya bayar ya zo a daidai lokacin da gwamnatin jihar Oyo ita ma ta umarci Fulani makiyaya da ke dazukanta da su bar wadannan yankuna, bisa zargin da ake yi mu su cewa ana samun baragurbi daga cikinsu da ke garkuwa da mutane.
Wannan lamari na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin makiyaya da wasu al’umomi da ke kudancin Najeriya saboda zargin da ake yi wa makiyayan da sace-sacen mutane domin karbar kudin fansa.
Sai dai makiyayan sun sha musanta wannan zargi suna masu cewa wasu gwamnatocin kudancin Najeirya suna yi musu kora-da-hali.
Ko da a makon jiya sai da kungiyar Fulani makiyaya ta Gan-Allah ta zargi jami’an tsaro na kungiyar sintiri ta Amotekun da kashe makiyaya hudu a farmakin da ta kai musu.
-Rahoton BBC Hausa