Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya mika sandunan mulki ga zababbun sarakunan Ezes 31 na al’ummomi daban-daban a jihar,Daily Post ta rahoto.
An gabatar da sandar mulkin ga iyayen gidan sarautar a dakin taro na Michael Okpara tare da dora musu alhakin wanzar da zaman lafiya da kare martabar al’adun yankunansu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanwo-Olu Ya Miƙa Sandar Mulki Ga Sabon Sarkin Masarautar Ogombo
Ikpeazu, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Ude Oko Chukwu, ya ce a yanzu an san su da kyau, bayan sun bi duk hanyoyin da ake bukata.
Ya tunatar da sabbin sarakunan gargajiyar bukatar su tabbatar da cewa an sasanta batutuwan da suka hada da iyakokin jama’a, filayen noma da sasanta rigingimu cikin lumana domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunansu daban-daban.
Ikpeazu ya yi amfani da dandalin wajen umurtar sarakunan da su yi amfani da nasarar hawan su kan karagar mulki domin kaiwa ga kowa da kowa da kuma neman hadin kai a duk inda ya dace don ba su damar samun nasara a mulkinsu.
A nasa jawabin, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Christopher Enweremadu, wanda ya shawarci sabbin sarakunan Ezes da su tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunansu daban-daban.
Sannan ya yabawa Gwamna Okezie Ikpeazu bisa yadda yake tafiyar da al’amuran jihar.
Da yake mayar da martani a madadin sarakunan, sarkin masarautar gargajiya ta Ugwu Nkpa mai cin gashin kanta a karamar hukumar Bende, Eze Princewill Onyegbu ya godewa gwamnan bisa karramawar da ya yi masu tare da gabatar musu da sandar mulaki.
Kazalika ya yi alkawarin cewa yankunansu daban-daban za su samu zaman lafiya da ci gaba mai dorewa
Sai dai kuma taron ya kusan gamuwa da cikas a yayin da ‘yan majalisar zartarwa na kungiyar kwadago ta Najeriya suka rufe babbar kofar dakin taron ta Michael Okpara a lokacin da ake aiwatar da yajin aikin.
Sarakunan gargajiya da magoya bayansu sun samu shiga dakin taron ne ta kofar baya.
A wani labarin kuma,Kwata-Kwata ‘Yan Najeriya Ba Su Yi Amanna Da Yan sanda ba– Shugaban Hukumar ‘Yan sanda
Shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda, Dakta Solomon Arase (IGP mai ritaya) ya dora laifin rashin samun nasarar gudanar da aikin ‘yan sandan al’umma a Najeriya a kan yadda ‘yan kasa ba su amince da ‘yan sanda ba.
“A Najeriya, ‘yan sanda sun yi wa kansu mummunan tabo inda ake ganin suna take hakkin bil’adama maimakon kare rayuka da dukiyoyi.