Gwamnan Jihar Rivers Nyessom Wike ya ce ko da wasa ba zai goyi bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba idan ya sake tsayawa takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC a babban zaben 2023.
Mista Wike wanda a baya ya rike mukamin Ministan Ilmi karkashin uban gidan nashi Jonathan ya ce babu ta yadda za a yi a ce ya juya baya wa jam’iyyar da ta mishi riga da wando ba wato PDP.
Tsohon Shugaba Jonathan dai cikakken dan jam’iyyar PDP ne to sai dai ana kishin-kishin din cewa yana iya yin hijira zuwa Jam’iyya mai mulki ta APCdon samun damar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Gwamna Wike ya ce ko da a baya ma dai shine ya yi uwa yayi makarbiya wajen samun nasarar Gwamnan Jihar Rivers din Rotimi Amaechi a shekara ta 2007.
“Ni cikakken dan Jam’iyyar APC ne, idan idan shugaba Goodluck Jonathan ya tsaya takara a PDP dole na zeb shi domin ba zan yi zagon kasa wa jam’iyya ta ba” Cewar Wike.
“To amma idan ya kuskura ya tsaya karakshin inuwar APC to ko da gigin wasa ba zan zabe shi ba sbaoda ba zan yi zagon kasa wa jam’iyya ta ba”.
Gwamna Wike ya kuma yi wani hsagube wa Ministan Sufuri Rotimi Amaechi bisa alakanta shi da wanda ya dauke shi aiki, to sai dai ya tunasar da shi cewa da ba don shi ba da bai zama gwamna a jihar Rivers ba a 2007.