Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa a Najeriya (PDP) a babban zaben kasar na 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi shaguben cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta na fakewa da sunan kame ta na sace mutane ta na yin garkuwa da su. Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a kafar sadarwarsa ta Tweeter a ranar karshen mako ranar Asabar, 3 ga Agusta, 2019, inda ya yi nuni da cewa, a na yi ne domin a tauye wa ’yan kasa hakkinsu na bayyana albarkacin bakinsu. A ta bakin tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, “shi ’yancin fadar albarkacin baki ba wai kawai kundin tsarin mulki ya tabbatar da shi ba ne kadai, a’a, ya na ma daga cikin wani ginshiki na shika-shikan dimukradiyya. Wannan sace mutane da a ke yi da sunan fakewa da kama su abin ki ne da allawadai.” Idan dai za a iya tunawa, a ranar da Atiku ya bada waccan sanarwar ne daidai da ranar da jami’an tsaro su ka cafke jagoran juyin-juyin-hali na #RebolutionNow, Mista Omoyele Sowere, wanda shi ne mawallafin jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters, wanda kuma shi ma dan takarar shugaban kasa ne a 2019. Bugu da kari, gabanin wannan lokaci ne a ka sace wani magoyin bayan daya daga cikin wadanda su ka nemi takarar shugabancin kasar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wato Abubakar Idris, wanda a ka fi sani da Dadiyata a yanar gizo. A rahotannin farko da a ka samu, jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian ta yi zargin cewa jami’an tsaro ne su ka kama shi, amma sun karyata rahoton hakan. A wata sanarwa kuma da dan takarar shugaban kasar na watan Fabrairun 2019 ya raba wa manema labarai a Abuja farkon makon nan ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Mista Paul Ibe, ya ce, ’yan Nijeriya su na rayuwa cikin matsanancin talauci tun daga ranar da Buhari ya zama shugaban kasa a shekarar 2015 har zuwa yau. Ya jaddada cewa, Najeriya ta na kara nutsewa cikin tekun talauci, cin hanci da rashawa da kin gaskiya a karkashin mulkin Shugaba Buhari. Atiku ya ce, rahoton Majalisar Dinkin Duniya ne ya kara fadakar da ’yan Nijeriya kan irin gararin da su ke ciki, saboda yadda gwamnatin Buhari ta nuna gazawa wurin gyara tattalin arzikin kasar. Rahoton ya ce, akwai ’yan Nijeriya miliyan 98 da ke rayuwa cikin matsanancin talauci. Don haka sai Atiku ya nuna tsananin mamakinsa kan yadda gwamnatin Buhari ta yi shakulaton bangaro da wannan rahoto. Koda ya ke a cikin dalilansa, ya na ganin cewa, gwamnatin ta Shugaban Najeriya Buhari ta yi biris da rahoton ne, saboda shi Atikun bai ce ta tafasa sauke a kai ba. “To, idan har abinda zai sa gwamatin Buhari ta zabura kan halin ni-‘ya-sun da ’yan Nijeriya su ke ciki shi ne ta ga Atiku ya sa baki, to, Atikun a shirye ya ke ya yi magana, don kare hakkin miliyoyin ’yan Nijeriya da ke fuskantar ukuba a karkashin wannan gwamnati,” in ji sanarwar dan takarar.