Gwamnatin Benue ta kafa kwamitin mika mulki
Gwamnatin jihar Benue ta kafa kwamitin mika mulki ga gwamnati mai jiran gado wanda aka shirya gudanarwa a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Samuel Ortom, Nathaniel Ikyur ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yanzu-Yanzu: Jam’iyar Labour Ta Lashe Kujerar Gwamna Na Farko A Najeriya
Ya ce an sanar da kafa kwamitin ne a taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar yau a gidan gwamnatin Benue da ke Makurdi.
Kwamitin mika mulki na karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Tony Ijohor, SAN.
Dukkan mambobin majalisar zartaswa ta Jiha mambobin kwamitin ne yayin da Daraktan zartarwa, Mista Bartholomew Aondoaver Ageraga, zai kasance sakataren kwamitin.
Ortom ya ce ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa cikin makonni uku.
A zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, Ortom ya zargi jami’an tsaro da canja zaben da aka yi a jihar.
Ya tuna yadda ake tursasa mutane da azabtarwa a wasu wurare yayin da jami’an tsaro suka kashe wasu
Ya ce jam’iyyar na nazarin sakamakon zaben kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar kuma nan ba da jimawa ba za ta bayyana wa al’umma matsayinta.
Ortom ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da zaman lafiya, ya kara da cewa gwamnatin sa ta ci gaba da jajircewa wajen ganin an samar da zaman lafiya.
A wani labarin kuma:Karancin Naira: NLC ta Umurci Ma’aikata su fara Zanga-zanga a Dukkan Ofisoshin CBN
Zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya tafi birnin Paris na kasar Faransa domin samun hutu da kuma tafiya kasa mai tsarki don gudanar da aikin hajji, in ji kakakinsa, Tunde Rahman.
Channels TV ta ruwaito cewa, “Bayan yakin neman zabe da kuma lokacin zabe, zababben shugaban kasa, Afro Bola Tinubu, ya tafi kasar waje domin hutawa da kuma tsara shirin mika mulki gabanin rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023,” in ji Rahman a wata sanarwa a ranar Laraba.