By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Borno ta hana kungiyoyi masu zaman kansu raba kayan abinci ko kayan agaji ga al’ummomin da aka tsugunar a jihar.
Wasu daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu sun ce matakin da aka dauka na iya kara ta’azzara rashin isasshen abinci a tsakanin al’ummomin da aka sake tsugunar dasu.
Haramcin wanda aka fitar a wata takarda mai dauke da kwanan watan 6 ga watan Disamba mai dauke da sa hannun Gwamna Babagana Zulum, an yi jawabi ne ga kungiyoyin jin kai da kuma abokan ci gaba.
Gwamnati a cikin sanarwar tace hana agaji ga al’ummomin da aka sake tsugunar da su wani bangare ne na kokarin “karfafawa mutane masu mutunci samun damar sayen abincin kan su”.
“Babu wata kungiya ta hadin gwiwa, ta gida, ta kasa da kasa da za a bari ta fara rabon kayan abinci da abubuwan da ba na abinci ba a kowace sabuwar al’ummarmu da aka sake tsugunar da su a fadin jihar.
“Ba za a ba da izinin rarraba abinci ba a sansanonin ‘yan gudun hijirar (IDPs) da kuma ‘yan gudun hijirar da ke cikin yankunan da suka karbi bakuncin a yanzu,” in ji sanarwar.