By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar EDO ta sanar da daukar matakin rufe makarantar sakandire ta Idogbo dake karamar hukumar Ikpoba-Okha a jihar, sakamakon lalata kadarorin makarantar da wasu dalibai da bata gari suka yi a ranar 2 ga watan Disamba.
Sakataren gwamnatin jihar, Mista Osarodion Ogie, a wata sanarwa da ya fitar a birnin Benin, a karshen mako, ya bayyana cewa: “An sanar da jama’a hakan ne domin jin ta bakin shugaban, malamai da daliban makarantar sakandare ta Idogbo, Ikpoba dake Karamar Hukumar Okha
“Bayan tashin hankalin daliban, wanda ya yi sanadin lalata kadarorin makarantar da wasu dalibai da ‘yan banga suka yi a ranar 2 ga Disamba, 2021, an rufe makarantar har sai an sanar da ranar dawowa.
“Rufe makarantar shine don baiwa gwamnatin jihar damar sanin matakin barnar da aka yi, gyara da kuma samar da hanyoyin da za a kaucewa sake afkuwar lamarin nan gaba.”