Gwamna Kayode Fayemi na Ekiti ya amince da rusa Majalisar gudanarwa ta Jami’ar Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Bamidele Olumilua, da ke Ikere-Ekiti (BOUEST).
Mista Yinka Oyebode, Babban Sakataren yada labarai na Gwamnan wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’ar nan a Ado-Ekiti, ya ce rushewa ya fara aiki nan take.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/gwamnatin-tarayya-ta-yi-alkawarin-tallafawa-manoma-da-kayan-aiki-na-zamani/
A cewar Oyebode, rugujewar ya yi daidai da tsarin mika mulki na jihar.
Ya ce Gwamna Fayemi ya gode wa shugaban hukumar da ‘yan majalisar kan gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jami’ar.
Oyebode ya kara da cewa “Gwamnan na yi musu fatan alheri a kan ayyukansu na gaba.”
(NAN)