By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Imo za ta gudanar da jana’izar mutanen da dama da suka mutu wadanda fashewar wata haramtacciyar matatar mai ta shafa da ke cikin dajin garin Abaezi ta afku a ranar Juma’a a karamar hukumar Ohaji Egbema a jihar.
Shugaban ayyuka na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa a jihar Ifeanyi Nnaji, ya ce ma’aikatun albarkatun man fetur da muhalli na jihar za su gudanar da jana’izar jama’ar da lamarin ya rutsa dasu.
Ya ce an tattara gawarwakin mutane sama da 100 da suka kone kuma suna jiran gwamnatin jihar za ta yi jana’izarsu.
A cewar jami’in hukumar ta NEMA, ba a tantance ko daya daga cikin wadanda abin ya shafa ba, domin sun yi konewar da ba a iya gane su ba
Nnaji ya ce, “Ma’aikatar albarkatun man fetur da muhalli ta jihar za ta gudanar da jana’izar jama’a ga wadanda abin ya shafa domin tuni gawarwakinsu ke rubewa.
“Kasuwa ce babba da ta hada mutane daga sassan kasar nan; kuma tunda sun kone ba a iya gane su, da wuya a gane su.
Sannan yace wani dangi ne kawai suka zo suka ga gawa guda daya, wanda suka ce yayi kama da nasu kuma suka dauke shi domin a binne shi kamar yadda aka saba.”
Comments 1