• Munyi nadin ne bisa duba can can ta da kwarewar aiki da kuma sadaukar wa da su ka nuna a kan aikin su
• Nadin zai fara aiki ne nan take.
• Wasu da basa tafiyar gwamna Badaru sun koka Kan wannan fadin.
A yunkirin ai watar da aikin ingantacce, kuma wada tace, gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ta amince da nada mutun 8 a matsayin sakatarori na dun-dun dun, a ma’aikatu daban da daban dake jihar.
A cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar, mai dauke da sa hannun babban mai baiwa gwamnan shawara akan kafafen yada labarai na Zamani, Auwalu Danladi Sankara ya ce, anyi nade naden ne, domin cike gurbi a ma’aikatu jihar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, nadin anyishi ne, bisa kwarewa da can-can ta, akan irin jajirce wa, da kuma sadaukar wa, da su ka nuna a kan aikin su.
Kazalika sanarwar ta bayyana sunayen wadanda a kai musu karin girman kamar haka: Hajiya Safiya I. Muhammad, Abdullahi Hassan, Lawan Muhammad Bello da Hajiya Uwani Jafar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani jami’in dan sandan ya kashe mutun 5.
Sauran sun hada da: Dr. Rabiu Miko, Abdullahi A. Mato, Nura Haruna da Dr. Haruna Usman. wanda sanarwar ta ce, karin girman na su, zai fara aiki ne nan take.
Sai dai jaridar Blueprint ta ruwaito cewa, wasu da aka tuntuba wadanda ba sa cikin tafiyar gwamna Badaru a siyasace, sun yi korafin cewa, nadin anyishi ne, ba bisa yin dubu na tsarin tarayya ba.
Sun kuma kara da cewa, wannan shine karo na uku, da a kayi irin wannan nadin, wanda ba a dauki wani dan bangaransu ba, duk da cewa sun can-can ta. Inda kuma su ka bayyana nadin a matsayin na nuna tafiyar tare.
Comments 1