Gwamnatin jihar Kano ta ce ta biya kimanin Naira miliyan 336 a matsayin kudin jarabawar NECO ta shekarar 2022 ga Hukumar da ke shirya jarabawar, kudin dalibai 29,031 a jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin a Kano.
Mista Garba ya yi wannan tsokaci ne a wani rahoto da kafafen yada labarai suka fitar da ke nuni da cewa daliban jihar ba za su iya tsallake jarabawar NECO ta shekarar 2022 saboda gazawar gwamnati wajen daidaita kudaden jarrabawar su.
Ya ce jerin daliba 15,313 da suka samu maki 9 a jarabawar cancantar ta, da dalibai 1,018 masu fama da nakasa.
“Kazalika, 7,300 don shiga tsakani na musamman wanda shine tushen ilimin yara mata, kuma kananan hukumomi sun biyawa dalibai 5,400”.
Malam Garba ya kuma ce ba yau (Litinin) aka fara jarrabawar ba.
Dimokuradiyya ta rawaito yana cewa “Yau ita ce “Test Interpretation Practical”, wato malamai su fito da hanyoyin da za a yi jarrabawar gwaji,” in ji shi.
NAN