By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar da ke kula da ma’aikata ta jihar Kwara za ta fara tattaunawa da ma’aikatan gwamnatin Wadanda za’a karawa matsayi na shekarar 2021 daga ranar 1 ga watan Nuwanba.
Shugabar Hukumar Kula da Ma’aikata ta jihar, Hajiya Habeebat Anike Yusuf ta bayyana haka a taron Hukumar.
Wata mai taimaka wa shugaban, Misis Bukola Shakirat Muritala, a cikin wata sanarwa, ta ce tattaunawar za ta shafi jami’an GL 07 zuwa GL 17 tsakanin ranakun Litinin zuwa Juma’a na kowane mako kuma za ta dauki tsawon kimanin makonni biyar (kwanakin aiki 25) tana gudanar da aikin.
Mataimakiyar ta ce, “Hukumar ta ba da shawarar cewa duk ma’aikatan da abin ya shafa su cika dukkan takardun da suka dace sannan su mika kwanaki hudu kafin ranar ganawar ta hannun jami’in ma’aikata na ma’aikatarsu da ma’aikatu da hukumominsu (MDAs) don gujewa bata lokaci ko kuma kai tsaye.za’a soke hirar ga duk wani jami’in da ya yi kuskure.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “ duk jami’an da abin ya shafa su zo da abin rufe fuska, Takaddun shaida na asali, da katin shaidar zama dan kasa,sai katin shaidar hidima, Amincewa da hutun karatu (idan akwai), Shaidar canza suna, takardar jarrabawa, Wasikar daukar aiki ta farko. Wasikar Gen. 40, Wasikar karin girmama ta Karshe, Wasikar Tabbatarwa da Takaddar yiwa kasa hidima NYSC ko keɓewa.
“Ta yi gargadin cewa Hukumar ba za ta fara wata hira ta gyara fuska ga duk dan takarar da ya rasa ranar hirar sa ba.”