Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti na musamman da zai bibiyi matsalar ambaliyar ruwa da ake fuskanta a kwanakin nan.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammadu Garba ya fitar ranar Litinin.
Muhammadu Garba ya ce gwamnatin Kano ta damu kwarai da ambaliyar da ake samu wadda ta haddasa matsaloli masu yawa a cikin birnin Kano.
KARANTA ANAN: Majalisar Dokokin Kano Zata binciki Musabbabin Wata Ambaliyar Ruwa A Jihar
Ya ce an dorawa kwamitin alhakin nazartar hanyoyin da ke cikin birni da kuma mugudanan ruwa da kwatoci domin gyarasu a kuma gina wasu idan da dama
Haka kuma kwamitin zai duba gine-ginen da aka yi akan magudanan ruwa da sune ke haddasa ambaliyar.
Kwamishinan ya kuma jajantawa al’ummar da sukayi asara mai yawa sakamakon ambaliyar.
Ya kuma ce jama’a su kara yiwa gwamnatin hakuri a cewarsa za a dauki matakin da ya dace domin magance matsalar.
DUBA WANNAN 👇👇👇
Atiku Ya Bada Tallafin Naira Miliyan 50 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Kano