Gwamnatin jihar Kano ta siyo injunan bugu takardu da sauran kayan aiki na miliyoyin naira domin inganta ayyukan hukumar kula da bunkasa ilimi ta Kano (KERD).
Da yake mika godiyar sa ga Gwamnan Jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa siyan kayan aikin, Daraktan Sashen Malam Abubakar Muhammad Kankarofi ya ce matakin zai ci gaba da habaka aiyuka na sashen buga takardu.
Ya bayyana cewa idan aka samar da sabbin injinan, sashin buga takardu zai samu sauki wajen buga jarrabawar cikin gida da sauran ayyuka.
Malam Kankarofi ya kuma yabawa kokarin tsohon kwamishinan ma’aikatar ilimi ta jihar Kano Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru wajen ganin an samu nasarar siyan kayayyakin.
Don haka ya tabbatar wa gwamnatin jihar cewa za a yi amfani da injinan cikin adalci da kuma ci gaban fannin ilimin jihar baki daya.
Injin bugun takardun da aka sayo sune injin sarrafa takarda A1 size, da Kord 64 Printing Machine da Polar yankan A2 Girman.
Sauran kayan aikin sun hada da na’urar daukar hoto goma, injin sikanin, guda 30 da sauran su.