ganduje 2

Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Biliyan 2.4 Domin Gyaran Makarantu 1, 180

Gwamnatin jihar Kano ta ware naira biliyan 2.4 domin gyaran makarantun Firamare da Sakandare har 1, 180 a fadin jihar. Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Talata a garin Kano a yayin bude taron kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki akan ilimin kananan makarantu da Sakandare a jihar.

‎Gwamnan ya ce sun ware naira biliyan 2.4 cikin shekara domin gyaran makarantun wanda ke dauke da dalibai 834,366. Sannan ya tabbatar da cewa; gwamnatin jihar ta kashe naira miliyan 318 domin ba da kayan makaranta kyauta ga dalibai 779, 522 ga sabbin daliban.

Sannan ya tabbatar da cewa; gwamnatin jihar za ta dauki Malamai 3, 000  domin ganin an bunkasa bangaren ilimi a jihar.

A cewar gwamnan akwai akalla yara miliyan takwas da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya, inda cikin wannan adadin akalla akwai yara miliyan daya daga Kano kawai. Ya ce abin takaicin shi ne kashi 57 cikin 100 na yaran da ba sa zuwa makarantan, mata ne. Kuma mafi yawansu suna jihohin arewa goma ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *