Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya taya shugaban Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu murnar cika shekara 60 a duniya.
Gwamnan ya taya Abdul Samad Rabiu murna ne a cikin takardar murnar da Sakataren watsa labaran gwamnan, Rafiu Ajakaye ya aika a garin Ilorin a ranar Talata a madadin gwamnan.
AbdulRazaq ya bayyana shugaban kamfanin BUA din a matsayin dan kasuwar Nijeriya da yake da kyakkyawan tarihi a bangaren kasuwanci da kuma kawo wa al’umma ci gaba.
A don haka gwamnan ya taya shi murna a madadin iyalai da gwamnatin Kwara. Gwamnan ya ce ya ji dadin yadda Kamfanin na BUA ya zama wanda ya fi kowa bayar da gudummawa ga jiha a yakin da ake yi da cutar annobar korona. Inda ya ce BUA ya bayar da naira miliyan 100 da kuma motocin asibiti uku a jihar domin yaki da korona.