Gwamnatin Najeriya za ta yi zama kan sabon mafi ƙarancin albashi a watan Maris – Minista
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na kasa Alhaji Mohammed Idris ya ce Gwamnatin Tarayya za ta fara tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi da kungiyoyin kwadago a watan Maris.
Idris ya bayyana hakan ne a wajen taron tattaunawa da kafafen Watsa Labarai karo na 21, da gabatar da kyautar gwarzon Afrika na shekarar 2023 da aka yi ranar Alhamis a Abuja.
Kungiyar Media Trust ce ta shirya wannan tattaunawar mai taken “Sake fasalin Tattalin Arziki a Gwamnatin Tinubu”.
Ya ce lokacin da aka cire tallafin man fetur, tun da farko shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin yin karin N25,000 cikin Al’bashi ga ma’aikata domin rage radadin cire tallafin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci Najeriya da ta baiwa ilimi fifiko a matsayin ginshiƙin zaman lafiya
Amma Ƙungiyar Ƙwadago ba ta gamsu ba, wanda hakan yasa Muka shiga tattaunawa da ita, bayan doguwar tattaunawa da su da Shugaba Tinubu muka cimma matsaya akan cewa mun amince da karin Naira 35,000 a kan Albashin.
Shugaban ya ce za a biya N35,000 na tsawon watanni shida don rage radadin cire tallafin man fetur wanda zai kasance daga Satumba 2023 zuwa Fabrairu 2024.
Don haka bayan an biya ladan albashi na wata shida;
a watan Maris Gwamnati da kungiyar kwadago za su sake haduwa don tattaunawa kan sabon mafi karancin albashin ma’aikatan.
Duk da haka yana da mahimmanci ‘yan Najeriya su fahimci manufar Tinubu na kokarin inganta walwala da jin daɗin duk ‘yan Najeriya, na san ba abu ne mai sauƙi ba amma ‘yan Najeriya za su ji daɗin idan shirin sa ya kammala.
“Ina so in yi kira ga ’yan Najeriya da su bai wa Shugaba Tinubu lokaci don gyara al’amura a kasar nan,” Idris ya jaddada.