- Gwamnatin jihar Neja ta rattaba hannu kan yarjejeniyar gina tituna mai tsawon kilomita 556 a fadin jihar da wani kamfani mai zaman kansa mai suna BENIJ Nigeria Limited
- Gwamna Bago yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar, ya ce matakin ya dace da tsarin sabunta birane na gwamnatinsa
- Titunan idan aka kammala su za su jawo hankalin masu zuba jari da kuma saukaka wa musu harkokin kasuwanci a jihar
Gwamnatin jihar Neja ta rattaba hannu kan yarjejeniyar gina tituna mai tsawon kilomita 556 a fadin jihar da wani kamfani mai zaman kansa mai suna BENIJ Nigeria Limited domin samar da ayyukan tuntuba.
Gwamna Muhammad Umar Bago yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar a masaukin gwamnatin jihar Neja da ke Abuja, ya ce matakin ya dace da tsarin sabunta birane na gwamnatinsa, kamar yadda Daily Post ta rawaito.
KARANTA WANNAN: Hankalin Gwamna Obaseki Ya Tashi Kan Zargin Gaje Kujerarsa Ko Ta Halin Kaka
Da yake kokawa kan matsalar karancin ababen more rayuwa, musamman tituna a jihar, Bago ya bayyana cewa: “Gwamnatina a shirye take ta sauya lamarin domin amfanin jama’a. Hanyoyin idan aka kammala su za su jawo hankalin masu zuba jari da kuma saukaka wa musu harkokin kasuwanci.”
A cewarsa, shigar da ayyukan kamfanin tuntuɓar shine don tabbatar da kula da inganci da ƙimar kuɗin da za a kashe kan ayyukan.
Ya bayyana cewa aikin titin mai tsawon kilomita 556 shi ne kashi na farko saboda ana sa ran za a gudanar da wasu ayyukan hanyoyin.
Da yake jawabi, babban mai ba da shawara a kamfanin BENIJ Nigeria Limited, Olatunji Ajayi, ya tabbatar wa gwamnatin jihar Neja cikakken kudurin ta na bayar da kwararrun da ake buƙata waɗanda za su tabbatar da samun inganci, ya ƙara da cewa kamfanin zai fito da cikakken tsarin ayyukan cikin makonni biyar.
Har ila yau, babban sakataren ma’aikatar ayyuka, Hassan Etsu ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar Neja yayin da Ajayi ya rattaba hannu a madadin kamfanin.
A wani labarin kuma, Kotu ta Daure Wani dan Kasuwa Bisa Laifin Aika Alat Na Bogi
Kotun Majistare dake zamanta a Jos a ranar Juma’a ta yanke wa wani dan kasuwa mai suna Samuel Jigede mai shekaru 35 hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari bisa samunsa da laifin aika sanarwar biyan kudi ta karya wato (fake alerts) bayan ya siya kaya.
Mai shari’a Shawomi Bokkos, ta yankewa Jigede hukuncin a takaice bayan ya amsa laifinsa.