Majalisar Dokoki ta buƙaci Gwamnati da ta kai ɗauki ga wadanda iftila’in ruwan sama ya shafa.
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta buƙaci Gwamnati da ta tallafawa al’ummar Ƙaramar Hukumar Dutsi ta jihar Katsina da ruwan sama yayi awon gaba da gidaje sama da guda Hamsin.
Ɗan Majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar ta Dutsi a Majalisar dokokin Jihar Honorabul Abduljalal Isma’il ne ya gabatar da ƙorafin a lokacin zaman majalisar.
Honorabul Abduljalal ya bayyana cewa, ruwan saman da ya share awoyi ana yi a daren asabar yayi awon gaba da gidaje da dabbobi da gonaki da wuraren kasuwanci da dama.
A cewar shi, ruwan ya tafi da gidaje kimanin guda 30 a garin Ɗan-Haune yayin da gidaje sama da 20 suke ruguje a cikin garin Dutsi.
Bisa haka Honorable Abduljalal yayi kira ga Majalisar da ta bukaci sashen Zartaswa da ya kai dauki ga al’ummar da abin ya shafa domin rage musu raɗaɗin abinda suka rasa.
Karanta wannan Labarin:Kotu ta Daure Wani dan Kasuwa Bisa Laifin Aika Alat Na Bogi
Haka kuma Majalisar Dokokin tayi kira ga sashen Zartaswa da ya kammala hanyar da ta tashi daga Garin Marabar-Ƙanƙara zuwa Ƙaramar Hukumar Ɗanja da ke Jihar Katsina mai tsawon kilomita 40.
Kiran ya biyo bayan koken da Ɗan Majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Ƙafur Honorabul Shu’aibu Wakili ya gabatar a zauren Majalisar.
Kamar yadda yace, tun shekarar 2020 Gwamnatin Jihar ta amince da gina Hanyar, kuma ya kamata a kammala ta tsawon watanni 6 amma daga bisani aka watsar da ita.
Mr. Wakili ya bayyana hanyar a matsayin mai muhimmanci duba da yadda za ta sauƙaƙe ma matafiya zuwa Kaduna, Abuja da ma wasu garuruwan.
Shugaban Majalisar Honorabul Nasiru Yahaya ya bada tabbacin cewa Majalisar za tayi dukkanin abinda ya dace domin ganin an tallafa ma al’ummomin yankin.
Daga karshe Majalisar ta bada umarnin aikewa sashen Zartaswa na Jihar da ƙudirorin a rubuce.
A wani labarin kuma:An gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a Jihar Katsina.
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya bayyana taron a matsayin mafi muhimmanci inda gwamnati ta haɗa kai da Malaman Addinin Musulunci domin gudanar da addu’ar neman daukin Allah maɗaukakin Sarki dangane da matsalar tsaron da ta addabi Jihar.
Gwamnan yace Matsalar tsaro ba nauyi ne na gwamnati kaɗai ba, akwai bukatar al’umma su jajirce matuƙa wajen gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya.