By Abbas Yakubu Yaura
Gobarar da ta tashi da sanyin safiyar Juma’a ta kone bututun mai na NNPC, Tuni dai jami’an NNPC da jami’an tsaro da jami’an kashe gobara dana NSCDC suka isa wurin domin bada agajin gaggawa tare ceto kan lamarin.
A cewar wani ganau, igiyar wutar lantarki ce ta ruguje ta fada kan bututun wanda a sanadiyyar haka ta haifar da tartsatsin wutar a ko’ina a yankin wanda ya kai ga zubar da mai na PMS dake kusa da yankin wanda ya kai ga kamawar bututun daga bisani ya fashe.
Wurin yana fuskantar matsalar lalata bututun mai saboda ayyukan barasa da ake gudanarwa.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas, Misis Adeseye Margret, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin da misalin karfe 8:30 na safe, ta ce, “muna sane kuma a halin da ake ciki a tashin gobarar bututun ta Baruwa.
Shugaban hukumar kashe gobara, wanda ya kasa bayyana ainihin musabbabin fashewar, yace binciken da hukumar ta gudanar zai bayyana musabbabin faruwar lamarin.