Gwamnatin jihar Sakkwato a ranar Asabar ta bayyana cewa za ta karbo bashin naira biliyan 65.7 daga lalitar cikin gida domin ganin ta kammala wadansu ayyukan ci gaba a jihar.
Gwamnatin ta ce za ta yi amfani da bashin wajen gudanar da ayyukan da suka shafi bunkasa ayyukan noma, gidaje, lafiya, ruwan sha, da bangaren shari’a.
Alhaji Mohammed Bello, mai bai wa gwamna Aminu Tambuwal shawara akan harkokin kafafen watsa labarai, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Mohammed Bello ya ce wannan matakin ya dace da kokarin da gwamnatin take yi wajen bunkasa walwalar ‘yan jihar.