Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa ta fara raba naira biliyan shidan da ta ware domin magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin mata da matasa, kamar yadda Sakataren gwamnatin, Alhaji Bala Bello ya tabbatar.
Bello ya bayyana hakan ne a garin Gusau a ranar Laraba, a yayin da ya karbi kayayyakin koyar da ayyukan yi da aka bai wa gwamnatin kyauta daga wata kungiyar da ba na gwamnati ba mai suna REACH, a wani shirinta na musamman.
Rahotanni sun tabbatar da cewa shirin na REACH shiri ne na shekara uku da ke samun tallafi daga ‘Global Affairs,’ dake Kanada, inda ‘Save the Children International’ ke kaddamarwa a tsakanin jihohi uku na arewa.
Sakataren gwamnatin ya ce gwamnatin jihar tuni ta bullo da shirin tallafawa mata da ayyukan yi a karkashin ofishin uwargidan matar gwamnan jihar, tare da bullo da shirin tallafawa matasa.
Ya kara da cewa; a karkashin shiri tallafawa mata da ayyuka yi, mata dubu 134, ne aka yi wa rijista, inda guda 6, 600 za su amfana da shirin har na tsawon shekara hudu. Ya ce kowanne daga cikinsu a karkashin shirin tallafawa mata za a rika ba ta naira dubu 20 duk wata. Inda kuma a karshen kowanne wata za a rika tallafawa mata 2, 800 a karkashin shirin.
Duk a cikin shirin, ya ce wasu dubu 6 da dari 600 suma za su rika amfana da naira dubu 10 a duk wata. Ya ce suna yin hakan ne domin rage marasa aikin yi a tsakanin matasa da mata da kuma wadanda ba su da karfi a jihar domin magance talauci da yake addabar jihar.